Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar.
Wakilai sun zabe shi ne daga gundumomin siyasa 147 na kananan hukumomi 14 na jihar
Fitowar Matawalle zai ba shi damar tsayawa takarar gwamnan jihar a karo na biyu a zaben 2023 mai zuwa.
Da yake bayyana Mista Matawalle a matsayin wanda ya lashe zaben, shugaban kwamitin zaben fidda gwani na gwamna a jihar, Babagana Tijjani-Banki, ya ce daga cikin wakilai 735, kuri’u 733 sun samu sahihin zabe.