Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya ayyana hutun mako guda, domin baiwa jama’a da ma’aikatan jihar damar yin rijista da kuma samun katin zabe na dindindin, PVC.
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, mai dauke da sa hannun Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Zamfara, Ibrahim Magaji Dosara, inda ya bayyana mako mai zuwa a matsayin kwanaki na kyauta don fara rajistar. In ji Gidan Talabijin na Channels.
“Wannan don sanar da jama’a cewa mai girma Gwamnan Jihar Zamfara Hon. Bello Mohammed Matawalle, MON (Shatiman Sokoto), ya ayyana mako mai zuwa (Litinin zuwa Juma’a) 20 zuwa 24 ga watan Yuni, 2022 a matsayin makon da babu aiki, domin baiwa jama’a da ma’aikatan gwamnati damar zuwa yankunansu domin yin rijista da kuma samun Katunan Zabe na dindindin, PVC, ”in ji sanarwar.
Wasikar ta kuma umurci manyan masu ruwa da tsaki na jihar da su ga an gudanar da aikin ba tare da wata matsala ba.