fidelitybank

Matawalle ka yi abun kunya na ɓatawa Bawa suna – Bwala

Date:

Wani mai taimaka wa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, ya yi tir da abin da ya bayyana a matsayin yunkurin bata wa shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta’annati, EFCC, Abdulrasheed Bawa.

Mai taimaka wa Atiku kan harkokin yada labarai, Daniel Bwala, ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani kan zargin Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara kan Bawa.

Matawalle dai ya zargi Bawa da rokonsa dala miliyan biyu.

A wata hira da BBC Hausa, gwamnan ya yi ikirarin cewa, a na bincikensa ne saboda “bai baiwa shugaban EFCC kudin da ya nema daga gare shi ba.”

Sai dai hukumar ta EFCC ta yi watsi da wannan ikirarin, inda ta jaddada cewa ba za ta shiga cikin fadan laka da wanda ake zargi da laifin cin hanci da rashawa da wawure dukiyar jihar sa ba.

Da yake mayar da martani kan lamarin, Bwala ya ce, yunkurin yiwa Bawa baki abin kunya ne.

Tweeting, Bwala ya rubuta: “Idan kuna son cire Bawa a matsayin shugaban EFCC, aƙalla ku kasance masu daraja game da shi kuma kuyi hakan cikin mutunci.

“Ra’ayin cewa ana binciken gwamnoni masu barin gado da ministocin gwamnati don haka ku sa daya daga cikin wadanda ake zargin ya yi masa kazafi, ko kadan, abin kunya ne.

“Bawa baya ga inganta nasarorin da Magu ya samu, ya kai hukumar zuwa wani kwararriyar kaya inda yake samun yabo daga nesa da kusa kuma ya cancanci girmamawa, ba zagi ba.

“Idan kuna da shaida a kansa, ku bi tsarin da ya dace na doka maimakon zagi.”

the nation newspaper nigeria today latest

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp