Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, tare da Babban Hafsan sojin kasar nan, Janar Christopher Musa, sun isa jihar Sokoto domin ba da gudummawa wajen murƙushe ƴan fashin daji da ke addabar yankin arewa maso yammacin ƙasar.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ne ya bai wa ministan da manyan hafsoshin tsaron ƙasar umarnin mayar da ayyukansu zuwa Sokoto bayan ƙaruwar ayyukan ƴan fashin daji a baya-bayan nan.
Duk da dai iƙirarin da gwamnatin Najeriya ke yi na cewar tana samun nasarori wajen yaƙi da matsalar tsaro da ake fama da ita a sassan ƙasar da dama, har yanzu dai ana ci gaba da samun kai hare hare.