Matatar mai ta Dangote da ke jihar Legas, ta fara tattaunawa da ƙasar Libya domin sayen ɗanyen man fetur da za ta dinga tace wa na ganga 650,000 a kullum.
Kamfanin labarai na Reuters ya kuma ruwaito cewa matatar, wadda attajiri mafi arziki a Afirka ya mallaka Aliko Dangote, tana yunƙurin sayo ɗanyen man daga ƙasar Angola.
Matakin na zuwa ne yayin da Dangote ke yunƙurin kauce wa ƙarancin man da yake fuskanta duk da ɗimbin arzikin man da Najeriya ke da shi, inda a gefe guda kuma hukumar kula da harkokin man ke zargin matatar da tace man dizel mara inganci.
A ranar Asabar da ta gabata ne Aliko ya faɗa bayyana cewa matatar tasa za ta fara tace ganga 550,000 ne a wannan shekarar, wanda kashi 85 cikin 100 ne kawai na ƙarfin matatar.
Sai dai ya ce dole sai sun ƙara yawan ɗanyen man da suke saya saboda ƙarancin wanda suke samu a cikin Najeriya.