fidelitybank

Matatar mai ta Dangote za ta fara samar da lita miliyan 25 na fetur kowace rana

Date:

Hukumar da ke sanya idanu kan harkokin man fetur ta Najeriya (NMDPRA), ta sanar da cewa sabuwar matatar mai ta Dangote za ta fara samar da lita miliyan 25 na man fetur a kowace rana ga kasuwannin Najeriya a cikin watan Satumbar da muke ciki.

Ana sa ran adadin man zai ƙaru zuwa lita miliyan 30 a kowace rana daga watan Oktoba.

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafin sada zumuntarta na X ta bayyana cewa, a wani taro da suka yi a Abuja ranar Talata, NMDPRA da Kamfanin NNPCL sun amince da fara sayar da ɗanyen mai ga matatar Dangote da kuɗin ƙasar wato Naira.

Bayan shafe sama da shekara guda da taƙaddamar da aikinta a watan Mayun 2023, matatar Dangote, a ranar Talata, ta fara fitar da man fetur ɗin.

A jiya ne dai kamfanin NNPCL ta ƙara farashin man fetur daga naira 617 zuwa naira 897.

Aliko Dangote ya ce da zarar kamfaninsa ya kammala shirye-shirye da NNPCL, man fetur na kamfanin zai shiga kasuwa.

uanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp