Matatar man Dangote za ta fara jigilar mai kyauta kuma kai tsaye ga gidajen mai a Najeriya daga yau, matakin da ake sa ran zai kawo sauyi a harkar man fetur ta ƙasar.
Kamfanin ya ce wannan shirin zai rage yawan masu shiga tsakani ya kuma ƙara inganci, tare da bai wa masu amfani da kuma gidajen mai damar samun zaɓuɓɓuka masu rahusa.
Matatar man Dangote dai mai ƙarfin tace ganga 650,000 na mai a rana ta fara aiki ne a shekarar 2023, inda ta taimaka wajen rage farashi bayan tashin gwauron zabin da ya biyo bayan cire tallafin mai da shugaba Tinubu yayi.