Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da ƙara farashin man fetur zuwa naira 955.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a kan ƙara farashin man, inda matatar ta ce za ta riƙa sayar da kowace lita a kan farashin naira 955 ga kwastomomin da za su saya tsakanin lita miliyan biyu zuwa lita miliyan 4.99.
Sai dai sanarwa ta ce masu sayan fetur ɗin da yawa daga lita miliyan zuwa sama, za su riƙa saya ne a kan naira 950, kamar yadda Daily Trsut ta ruwaito.