Kamar yadda muka kawo muku rahotannin abubuwan da suke faruwa a Moroko sakamakon girgizar ƙasa da ta faru a tsaunin Atlas Moutain – da yawa mutane sun rasa masoyansu.
Lahcen ya shiga ciki mummunan tashin hankali bayan matarsa da ‘ya’yansa huɗu sun mutu a wannan musiba.
Ya shaida wa AFP cewa “Na yi asarar komai. Babu abin da zan iya yi a yanzu, so nake na bar duniyar baki ɗaya saboda baƙin ciki.”
Ana ta gina kabarurruka a saman tsaunukan domin rufe gawarwaki.
Hasna, wadda itama mazauniyar yankin ce ta ce “duka ƙauyen na makokin ‘yan’yansu da suka mutu”. In ji BBC.


