fidelitybank

Matashin da ya yaga Kur’ani a Kano ya shiga hannun hukuma

Date:

Wani matashi maigadi wanda har yanzu ba a san sunansa ba, ya shiga hannun jami’an ‘yan sandan jihar Kano, sakamakon zarginsa da a ke yi da yaga littafi mai tsarki na Kur’ani tare da take wani sashinsa.

Wanda ake zargin, ya kubuta daga yunkurin babbaka shi da rai da jama’ar yankin Kuntau a birnin Kano suka yi niyya, bayan isar jami’an hukumar Hisbah wurin da lamarin ya faru a ranar Lahadi.

Daga bisani jami’an Hisbah sun mika shi hannun ‘yan sanda, kuma a halin yanzu an tsare shi inda ake ci gaba da bincike a kan shi.

Daily Trust ta rawaito cewa, wani É—an uwan mamallakin gidan da matashin ke gadi mai suna, Sunusi Ashiru, ya ce, da kyar matashin ya kubuta daga hannun jama’a.

Ya ce: “Ba na nan lokacin da ya aikata, amma na dawo na tarar da jama’a dauke da makamai daban-daban suna kokarin halaka shi. Na tambaya, sun yi min bayanin abinda ya yi, kuma a lokacin ne jami’an hukumar Hisbah suka kama shi tare da mika shi hannun ‘yan sanda.”

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da aukuwar lamarin, kuma ya ce, wanda ake zargin ya na hannun su tare da ci gaba da gudanar da bincike a kan shi.

sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp