fidelitybank

Matashin da ya shiga aikin DSS da takardar jabu ya rataye kansa a Kano

Date:

Wani matashi mai kimanin shekaru 29 mai suna, Bashir Ibrahim, ya hallaka kansa har lahira ta hanyar rataye kansa a unguwar Hagagawa dake karamar hukumar Bichi a jihar Kano.

Kadaura24 ta rawaito matashin a na hasashen ya kashe kansa ne saboda karar shi daga aiki da hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta yi, sakamakon samun sa da akai da shaida karatun NCE ta Jabu.
” Da ma ya shiga aikin ne na DSS da takardar NCE ta Jabu, su Kuma suka yi bincike har suka gano shi , to shi ne fa suka kore shi daga aiki” . Inji Majiyar Kadaura24
Lokacin da kadaura24 ta zanta da wani dan uwan mamacin wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace tun lokacin da aka sallami mamacin daga aiki ya shiga damu wanda suna zaton hakan ne yasa Bashir ya rataye kansa.
” Duk da yake bai fadawa kowa cewa zai kashe kansa ko dalilin da yasa ya hallaka kansa ba, sannan kuma bai ajiye wata alama ko dalilin da yasa ya aika hakan ba , Amma dai muna ganin yayi hakan ne sakamakon korar sa da akai daga aiki da kusan  makwanni uku da suka gabata”.
Dan Uwan mamacin ya ce tuni dai akai jana’izar mamacin kamar yadda addinin musulunci ya tanada da misalin karfe 9 na daren jiya Alhamis a garin Bichi dake jihar kano.

breaking news in nigeria today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp