fidelitybank

Matashin da ya kwakulewa yaro ido a Kano ya shiga hannu

Date:

Rundunar ƴan sandan Kano ta tabbatar da kama wata tsohuwa da ake zargin ta saka wani matashi mai shekara 17 ya ƙwaƙulewa wani yaro mai suna Mustapha Dahiru ido don a haɗa musu layar zana.

Rundunar ƴan sanda ta ce ta kamo matar ne bayan koke da suka samu daga jama’ar unguwa da ƴan sa kai na yankin unguwar Dan Tsinke a karamar hukumar Tarauni a Kano.

Tun kafin ƴan sanda su kai ga kamo matar da ake zargi da sa matashin ya cirewa yaron ido, kungiyar tsaro ta ‘yan sa-kai ta Dan Tsinke da ke kusa da Unguwar Sheka suka kamo matashin da ake zargi da cirewa yaron ido ɗan shekaru 10-11.

Matashin da ake zargi ya shaida musu cewar wata tsohuwa ce ta umarci da ya kawo mata ido don ta hada masa layar zana, kamar yadda Rabi’u Suleiman Mai Matasa mataimakin sakatare na kungiyar ‘yan-sa kai ta Dan Tsinke a Kano ya shaidawa BBC.

SP Abdullahi Kiyawa kakakin ƴan sanda a Kano ya tabbatar da faruwar al’amarin, ya kuma ja hankulan al’umma da su ringa sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a kewayen su, don kaucewa afkuwar irin wannan lamari.

Ko a makon da ya gabata sai da aka sami waji matashi da ya tura ‘yar uwarsa a cikin rijiya, a yankin karamar hukumar Rimin Gado a Kano, tare da wani matashi da ya kashe wata yarinya, yar makwabcin gidansu, bayan da ya nemi kudin fansa.

vanguard newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp