Matashin da ya banka wa masallaci wuta tare da masallata a jihar nan, ya amsa laifin da ake tuhumar sa da aikatawa a gaban kotu.
Matashin mai shekara 39 wanda ya gurfana a gaban kotun shari’ar musulunci dake unguwar Danbare a karamar hukumar Kumbotso, karkashin jagoranci Alkali Halhalatul Kuza’I Zakariyya, ana tuhumarsa da laifuka uku, ya ce ya amince da tuhume-tuhumen da aka karanta masa.
A ranar Laraba 15 ga watan Mayu ne matashin ya cinna wuta a wani masallaci da ke ƙaramar hukumar Gezawa, daidai lokacin da ake sallar asuba.
Yanzu haka mutane da dama ne suka rasa rayukansu sanadiyyar wutar, yayin da wasu mutane 12 ke kwance a asibiti.
Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa 31 ga wanna watan, domin bai wa wanda ake zargi damar samun lauya, sannan masu gabatar da kara su samu damar tattara shaidun su.