Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta tabbatar da cafke wani Bashiru Ahmed, bisa zargin datse kunnen wani abokinsa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar da kamen a ranar Laraba, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin a wata mayankar da ke unguwar Agege a Legas.
Ya ce wanda ake zargin ya yanke kunnen Abdulahi Adulmalik kan rashin fahimtar juna da suka yi a shekarar 2023.
“Wani Abdullahi Adulmalik na Kasuwar Abattoir ne ya kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Abattoir a ranar Litinin.
“Mai karar ya ce da misalin karfe 4:00 na safiyar wannan rana, wani Bashiru Ahmed, wanda ke Kasuwar Abattoir, ya yi amfani da wuka ya yanke masa kunnen dama saboda rashin fahimtar da suka yi a shekarar 2023.
“An garzaya da wanda aka kashe zuwa asibiti inda ake ci gaba da kula da shi,” inji shi.
Hundeyin ya ce ana tsare da wanda ake zargin ne domin yi masa tambayoyi.