fidelitybank

Matashi ya shiga hannun hukuma bayan zargin kisan kai a Kano

Date:

Rundunar ƴansandan jihar Kano ta ce ta kama wani matashi bisa zargin kashe saurayin ƙanwarsa a lokacin da ya je zance gidansa.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ya ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Kunya da ke yankin ƙaramar hukumar Minjibir.

Sanarwar yansandan ta ce matashin wanda ɗan asalin ƙauyen Goda, ya je Kunya ne wajen budurwarsa domin zance, sai dai jim kaɗan bayan zuwan nasa sai aka yi zargin cewa yayan budurwar mai suna Mansur Umar mai shekara 25 ya doke shi da sanda a ka, lamarin da ya haddasa masa munanan raunuka.

”Tuni aka garzaya da shi asibitin Kunya daga baya kuma aka mayar da shi asibitin Murtala domin ba shi kulawar gaggawa, inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsa”, a cewar ƴansandan.

Ƴansanda sun ce tuni suka kama Mansur, domin gudanar da bincike a sashen binciken manyan laifuka na rundunar ƴansandan jihar.

Rundunar ƴansandan ta yi kira ga jama’a su riƙa sanya haƙuri a cikin al’amuransu, tare da kai rahoton duk wata jayayya da aka samu tsakanin wasu mutane zuwa ofishin ƴansanda mafi kusa.

opra news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Buhari ya yi wa Najeriya hidimar da ba za a manta da shi ba – António Guterres

Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres...

Binani ta koma jam’iyyar haɗaka ta ADC

'Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu...

A Talata zan koma aiki na a majalisa – Natasha

Yar majalisar Dattawa, Sanata Natasha Akpoti, ta ci alwashin...

An sake mayar da yan Najeriya 294 gida daga Nijar

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta...

An gano motoci 35 da aka sace a wata shida

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa a Najeriya ta ce...

Shugaban Laberiya ya je ta’aziyyar Buhari a Monrovia

Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar...

Rundunar Yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar...

Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan Mutane 3

Hukumomi a Iran sun zartar wa mutum uku hukuncin...

Ƴansanda sun kama ƙasurgumin ɗanbindiga a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce, jami'an ta sun...

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...
X whatsapp