fidelitybank

Matashi ya sha kwaya ya mutu a ranar murnar haihuwarsa

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas, ta tabbatar da mutuwar wani matashi mai shekaru 21 mai suna Micheal Arigbabuwo, wanda ya rasa ransa a wajen bikin zagayowar ranar haihuwarsa, bayan da aka zarge shi da hada wasu kwayoyi masu tsauri guda biyu don yin tasiri.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda (PPRO) a jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Hundeyin wanda ya tabbatar da kame uku daga cikin abokan mamacin ya ce, lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a unguwar Ikorodu da ke jihar Legas.

Ya ce bayanan da ‘yan sanda suka samu a Ikorodu sun nuna cewa da misalin karfe 7:30 na yammacin ranar Juma’a ne, aka yi kira da nuna damuwa cewa wasu ‘yan kungiyar Yahoo Yahoo sun kawo gawa zuwa yankin Igbogbo da ke Ikorodu.

“Bisa bayanin, gungun masu binciken sun ziyarci inda lamarin ya faru kuma suka dauki hoto. An kama wasu matasa uku masu shekaru 23 da 24.

“Wadanda ake zargin sun yi ikirarin cewa marigayin ya sha hayaki da karfi kuma ya sha codeine a wajen bikin zagayowar ranar haihuwar daya daga cikin abokansu da aka gudanar a yankin Igbogbo a Ikorodu.

“Wadanda ake zargin sun kara da cewa marigayin ya fara haki. An garzaya da shi asibiti amma ya mutu,” inji shi.

Hundeyin ya kara da cewa an kwashe gawar an ajiye ta a babban asibitin Ikorodu domin a tantance gawar.

Don haka ya gargadi matasa kan shaye-shayen miyagun kwayoyi, yana mai jaddada cewa, miyagun kwayoyi za su kawo karshen rayuwarsu cikin bala’i.

today daily post news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp