An kama wani matashi mai matsakaicin shekaru da ake zargin barayi ne a yankin Osiri da ke Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.
An tattaro cewa wanda ake zargin ya mutu ne a daren ranar Talata a lokacin da yake kokarin satar na’urar taransifoma a yankin.
Ana zargin wanda aka kashe din ya je ya yi sata a na’urar taranfoma ne kafin a dawo da wutar lantarki kuma ya makale.
Wata majiya da ba ta so a wallafa sunansa a cewar Daily Post, ta ce mutanen yankin sun farka da safiyar yau Laraba, domin ganin gawar mamacin kwance a cikin magudanar ruwa.
Ya ce: “A yau mun tashi ganin gawar wani matashi a na’urar taransifoma a kewayen titin Osiri.
“Ya yi nasarar yanke biyu daga cikin igiyoyin amma ba zato ba tsammani ya gamu da ajalinsa a lokacin da haske ya zo yankin.”