Rundunar ‘yan sanda reshen Ovwian/Aladja dake karamar hukumar Udu a jihar Delta, ta cafke wani matashi mai suna Samuel, bayan abokinsa (wani matashi) ya mutu a gidansa bisa zarginsa da shan wani magani da ake zargin tramadol ne.
Lamarin ya faru ne a titin Okuku, unguwar Ovwian a karamar hukumar Udu, kamar yadda jaridar DAILY POST ta ruwaito.
An bayyana cewa wanda ake zargin ya sayi magungunan da yawa wanda ya sha tare da marigayin kafin ya je wasan kwallon kafa a unguwar ya bar abokinsa a gidan.
Da isowar sa daga filin sai ya hadu da abokinsa a sume a gidan. Ya ɗaga ƙararrawa amma wata ma’aikaciyar jinya a kusa ta tabbatar ya mutu.
Karanta Wannan: Mutane 37 a ka yanke wa hukunci a Kano – NDLEA
Makwabtan wanda ake zargin da mazauna yankin da suka yi magana a boye sun ce shan miyagun kwayoyi da kuma rashin da’a na ‘yan biyun ya yi yawa a yankin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe a zantawar da wakilinmu ta wayar tarho, ya ce rundunar ‘yan sandan ba za ta ce uffan ba a kan lamarin a yanzu, domin iyayen wadanda suka rasu ba su shirya taimaka wa ‘yan sanda da bayanai ba.
Wanda ake zargin yana cikin sanyin jiki a sashin ‘yan sanda a lokacin da wannan rahoto ya fito