fidelitybank

Matashi ya kashe kishiyar mahaifiyarsa da dan ta a Kano

Date:

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano, ta kama wani matashi dan shekara 20, Ghadaffi Sagir, bisa zargin kashe kishiyar mahaifiyarsa Malama Rabi da dan ta.

Kakakin rundunar, SP. Abdullahi Kiyawa ya tabbatarwa da manema labarai faruwar lamarin.

Ya ce, lamarin ya faru ne a daren Asabar da misalin karfe 11:00 na dare a Rijiyar Zaki daura da Layin Dorawan ‘yan Kifi a karamar hukumar Ungogo.

Ya bayyana cewa wanda ake zargin ya yi amfani da wani abu mai kaifi, inda ya yanka mahaifiyar tasa sannan ya shake yarta har lahira.

Kiyawa ya ce an kama wanda ake zargin kuma ya amsa laifinsa.

Ya ce ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike kan laifin.

Bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya kashe mahaifiyarsa, Malama Rabi bisa zarginsa da haddasa rabuwa tsakanin mahaifiyarsa da mahaifinsa.

Shi ma wanda ake zargin ya kashe diyar ne saboda ta ga ya kashe mahaifiyarsa.

legit nig. news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp