Kotun Majistire ta garƙame wani mutumi ɗan kimanin shekara 42, Oluwafemi Olaifa, a gidan gyaran hali dake Ado-Eikiti, jihar Ekiti, bisa zargin kashe abokinsa.
Daily Trust ta rawaito cewa, mai gabatar da kara, Insufekta Olubu Apata, ya shaida wa kotu cewa mutumin ya aikata laifin da ake tuhumarsa ranar 20 ga watan Fabrairu.
Sifeta Apata na hukumar yan sanda ta jihar Ekiti ya faɗa wa Alkali cewa wanda ake zargi ya halaka wani mutumi mai suna, Ayoola Ajayi.
Apata yace a jawabin da Mutumin ya yi wa yan sanda, ya nuna cewa mamacin babban abokinsa ne kuma amininsa, kuma a ranar sun haɗu a wurin mai POS dukansu sun je cire kudi.