fidelitybank

Matasan da suka fusata sun sa an goge shafin Facebook na Rarara a kan waƙar Tinubu

Date:

Bayanai na cewa an goge shafin fitaccen mawaƙin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara daga dandalin Facebook

Hakan na zuwa ne bayan da aka yi zargin cewa wasu masu amfani da dandalin ne suka riƙa kai ƙorafin shafin nasa ga kamfanin na Facebook,(reporting) bayan ya wallafa wata sabuwar waƙa a shafin nasa da ake zargin ba ta yi wa matasan daɗi ba.

A ‘yan kwanakin nan ne dai mawakin ya fitar da wata sabuwar waƙa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta.

Waƙar dai ta ƙunshi yabo ga shugaban Najeriya, Bola Tinubu kan wasu ayyukan da mawaƙin ke iƙirarin shugaban ya samar wa ƙasar.

An ji yo Rarara cikin wasu baitocin wakar na cewa:

“Tinumbu ya gama mana aiki ba batun ɓoyo,

”yanzu talauci ƙyaram, yunwa ƙyaram,

”kana security daram-dam-dam, ƴanci daram,

”Sannu farin cikin ƙasa Tinubu, sai godiya, baba makaniken gyara lamba ɗaya”.

Sabuwar waƙar na zuwa ne a daidai lokacin da wasu matasan ƙasar ke shirin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa da yunwa da rashin tsaro da ƙasar ke fama da su.

Wannan dalilin ne ya sa suke kallon waƙar tamkar izgili ko zolaya mawaƙin ke yi wa ‘yan ƙasar, lamarin da ya sa suka ɗauki matakin gangamin kai ƙorafin shafin nasa zuwa ga kamfanin Facebook, domin buƙatar kamfanin ya goge shafin.

Bayan kamar kwana biyu da fara gangamin, Facebook ya goge shafin – mai mabiya fiye da miliyan guda daga dandalin. In ji BBC.

bbc news nigeria today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...
X whatsapp