Wasu matasa da suka fusata suka fito kan titunan Maiduguri, babban birnin jihar Borno, domin nuna rashin jin dadinsu da shahararren mawakin nan, Davido wanda ya wallafa wani faifan bidiyo na cin zarafin addinin Musulunci a shafinsa na Twitter.
Davido ya fuskanci suka sosai bayan ya raba faifan bidiyon wakar na mai sa hannun sa, Logos Olori sabuwar wakar ‘Jaye Lo’ wacce ta kama mutane suna addu’a da rawa a gaban masallaci.
Fitattun Musulman Najeriya da dama da suka hada da tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, Sanata Shehu Sani, jarumi Ali Nuhu, sun nemi Davido da ya sauke faifan bidiyon tare da neman gafarar musulmi kan “rashin daraja” addininsu.
Daga karshe mawakin ya sunkuyar da kansa lamba bayan sa’o’i 48 kuma ya goge bidiyon da ya janyo cece-kuce.
Sai dai Davido bai nemi afuwa ba kan matakin da ya dauka.
A fusace da girman kan sa wasu matasa musulmi a Maiduguri suka fito kan titi suna cinna wa babbar tutar mawakin wuta.
A wani faifan bidiyo da ke zagayawa a shafukan sada zumunta, an kama matasan a bainar jama’a