Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), ta bayyana cewa, matasan Najeriya ne suka jagoranci kididdigar alkalumma don kammala sabbin rajistar katin zabe a 6,081,456, daga cikin jimillar 10,487,972.
INEC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar Litinin, inda ta bayyana sabbin rajistar katin zabe da misalin karfe 7 na safe a ranar Litinin, 27 ga watan Yuni.
Hakan na zuwa ne bayan da hukumar ta amince a makon da ya gabata na tsawaita aikin rajistar masu kada kuri’a na tsawon kwanaki 60 kamar yadda kotu ta yanke a baya-bayan nan.