Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya shawarci matasa da su guji shiga banga a zabe mai zuwa yayin da aka fara yakin neman zabe.
Sarkin ya ba da wannan shawarar ne a ranar Asabar a lokacin da ya jagoranci taron addu’o’i ga kasar a wani bangare na ayyukan da Masarautar ta shirya domin tunawa da cikar kasar shekaru 62 da samun ‘yancin kai.
Ya kuma gargade su (matasa) da ka da su bari ‘yan siyasa su yi amfani da su wajen biyan bukatunsu na son kai, inda ya bukace su da su guji aikata ayyukan da za su iya haifar da tashin hankali a jihar musamman ma kasa baki daya.
“Ina so in yi amfani da wannan damar domin yin kira ga matasa da su guji ‘yan daba su guje wa ayyukan da za su iya haifar da tashin hankali a lokacin zabe,” in ji Sarkin.
Sarkin ya kuma yi kira ga ‘yan siyasa a kasar da su daina yin kalamai marasa gadi da kalaman nuna kiyayya a lokacin yakin neman zabe.
Ya ce an yanke shawarar shirya tarukan addu’o’in ne da nufin neman taimakon Allah don ganin an gudanar da zabe cikin lumana a kasar nan a 2023.
“An shirya taron addu’o’in ne domin yi wa kasa addu’a a daidai lokacin da ake bikin cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai domin ganin an gudanar da zaben 2023 cikin nasara,” inji Bayero.
Sarkin ya bayyana fatan ’yan siyasa za su yi amfani da shawarar da dattawa da malamai daban-daban suke ba su wajen gujewa duk wani abu da zai zafafa harkokin siyasa.
Taron addu’ar ya samu halartar ‘yan majalisar Masarautar da kuma sauran masu hannu da shuni daga sassa daban-daban na jihar.