Wasu matasa biyu sun amsa cewa, sun yi allurar pentalin fiye da kima a kan wani dan direban babur mai ƙafa uku tare da dauke masa babur da
Wadanda ake zargin, Habu Badiru mai shekaru 27 da Auwal Lawan mai shekaru 26, masu sana’ar sayar da magunguna, sun amsa laifin kashe Algoni Goni tare da jefa shi kogin Uba a jihar Adamawa, ta hanyar yi masa allura maganin pentalin da ya wuce gona da iri tare da kwace masa babur ɗin sa.
Mutanen biyu sun yi ikirarin cewa, sun kashe Goni ne a ranar 4 ga Maris, 2022, sannan suka jefar da gawarsa a cikin wani kogi da ke Uba, karamar hukumar Hong, daga nan ne Habu ya hau babur din zuwa Mubi ya sayar da shi.
Wadanda ake zargin sun bayyana cewa, sun bi babur din Goni ne, domin su tara wa Habu Naira 100,000, domin ya biya bashin da ake bin sa.