Uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga mata masu juna biyu su dauki zuwa asibiti domin duba lafiyarsu da muhimmanci, da yin gwajin cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV.
Sanata Remi ta ce wannna zai bai wa jami’an lafiya damar bin hanyoyin kare jaririn da ke cikin uwa daga kamuwa da cutar, da tabbatar da ingancin lafiyar uwa da jaririnta.
Misis Remi ta bayyana hakan ne a wata ziyara da ta kai Babban asibitin gwamnatin Tarayya da ke Abuja, inda ta tarbi jaririn farko da aka haifa a wannan sabuwar shekarar ta 2024.
Ta kuma yi kira ga masu hannu da shuni su shiga a dama da su wajen taimakawa gwamnati na cika burin samar da ingantaccen fannin lafiya ga ‘yan Najeriya baki daya.