Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Oluremi Tinubu ta jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Jigawa kan fashewar tankar mai a garin Majiya da ke karamar hukumar Taura, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 90.
Uwargidan shugaban kasar ta cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ta yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki da ya baiwa Aljanah Fridaus ga wadanda suka rasu ya kuma jajantawa duk wadanda wannan bala’i ya shafa.
Ta ce, “Ina mika ta’aziyya ga Gwamnan Jihar Jigawa, Mai Girma, Malam Umar Namadi da al’ummar Jihar bisa rashin dacewar fashewar tankar tanka da ta afku a ranar Laraba, 16 ga Oktoba, 2024.
“Wannan mummunan al’amari da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, da jikkata wasu da asarar dukiyoyi, abin takaici ne.
Tunanina da addu’a na tare da ku a wannan lokaci.
“Ina rokon Allah ya baiwa abokai, iyalai da kuma masoyan rayukan da suka rasu ya ba su ikon jure rashi mai raÉ—aÉ—i, ya kuma basu lafiya cikin gaggawa.”