Mai ɗakin gwamnan jihar Akwa Ibom, Patience Umo Eno ta mutu.
Cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ini Ememobong ya fitar, ranar Juma’a ya ce ta mutu ne ranar Alhamis.
Sanarwar ta ƙara da cewa marigayiyar ta rasu ne a gaban iyalai da danginta.