‘Yan sandan Kenya sun kama wata mata da ake zargi da jefa jaririyarta ƴar watanni takwas a cikin tekun Indiya ranar Lahadi.
Shaidu sun shaida wa kafafen yaɗa labaran kasar cewa, matar ta jefa jaririyar ne cikin teku daga wani jirgin ruwa a lokacin da ya doshi garin Mombasa da ke gaɓar teku.
Bidiyon yadda ake ceto jaririyar ya karaɗe shafukan sada zumunta, lamarin da ya sa al’ummar Kenya da dama ke nuna ɓacin ransu ga matar da kuma jin dadin yadda aka ceto jinjirar.
“An garzaya da jaririyar don ba da agajin farko a cibiyar agaji ta Red Cross, inda aka kula da ita sannan aka sallame ta cikin yanayi mai kyau, an kuma kai mahaifiyarta ofishin ‘yan sanda domin yi mata tambayoyi.” kamar yadda kafafen yaɗa laarai na K24 da Citizen TV suka ruaito.
Tun farko ƙungiyar agaji ta Red Cross ta Kenya ta ce jariririyar tana cikin ƙoshin lafiya a cibiyarta ta agaji.
Har yanzu dai ba a bayyana ko irin tuhume-tuhumen da za a yi wa matar ba. In ji BBC.


