Wata matar aure mai matsakaicin shekaru, Sadiya, wacce mijinta ya tsare ta da yunwa tsawon shekara guda a garin Nguru da ke jihar Yobe, rahotanni sun bayyana cewa ta mutu a asibiti.
Rahotanni sun bayyana cewa, Sadiya ta rasu ne a ranar Asabar a Kano, yayin da take jinya a asibitin koyarwa na Aminu Kano.
Mahaifiyar Sadiya mai yara hudu, mahaifiyarta Hadiza ce ta kubutar da ita bayan da ta yi zargin a duk lokacin da ta yi kokarin ganawa da diyarta ta waya sai ta ji Muryar ta ta sauya.
Idan dai za a iya tunawa, rundunar ‘yan sandan jihar Yobe a yayin da take aiki da sammacin da babbar kotun majistare ta Nguru ta bayar, ta tabbatar da cafke mijin Sadiya, Ibrahim Yunusa bisa zargin tsare matarsa da kuma kashe ta da yunwa.
“Ba a san dalilin yin wannan aika-aika ba, amma ‘yan sanda sun kama Mista Ibrahim Yunusa tare da mika shi ga kotun majistare,” DSP Dungus ya tabbatar.
Bayan faruwar wannan lamari na cin mutuncin wanda abin ya shafa, an gano cewa gamayyar kungiyoyin kare hakkin mata da kananan yara 56 sun hada karfi da karfe domin ci gaba da shari’ar har sai an yi adalci ga wanda lamarin ya shafa.