fidelitybank

Matar da masu fashin jirgin ƙasa suka yi garkuwa da ita ta haihu a hannun su

Date:

Guda daga cikin fasinjojin da ‘yan fashin daji suka sace daga jirgin kasan da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris, ta haihu a hannun masu garkuwa da ita.

Tashar talabijin ta AriseTV, wadda ta wallafa wannan labarin, ta kuma ce wani dan uwan matar ne ya sanar da su haka.

Dan uwa nata ya sanar cewa, an kai wani likita wurin da ake rike da ita wanda ya taimaka mata wajen haihuwa.

“Matar na da tsohon ciki wanda ya kai wata takwas yayin da aka sace ta da sauran gomman fasinjoji, kuma ta haihu ne bayan da ‘yan ta’addan suka gayyaci likitoci su karbi haihuwar. Sai dai ba mu san halin da abin da ta haifa yake ba,” in ji dan uwan matar.

A farkon wannan makon ne dai masu garkuwa da mutanen suka wallafa hotunan fasinjojin da kawo yanzu suka shafe wata guda cur a hannunsu.

nigeria news(punch)

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp