An gurfanar da wata mata Adenike Okunbanjo mai shekara 60 a gaban Kotun Majistare da ke jihar Lagos, kan zarginta da satar wayoyin iPhone har 99 da kudinsu ya kai naira miliyan 14.85.
A cewar jridar Guardian, matar da ake zargi ɗin ƴar kasuwa ce.
Lauyan da ke tuhumar ta ASAP Raji Akeem, ya gaya wa kotun cewa ta yi wannan laifi ne ranar 16 ga watan Junairun 2017 a tashar jirgin saman Murtala Muhammed da ke Lagos.
Akeem ya bayyana cewa darajar iPhone din sun kai naira miliyan 14.85, kuma wani Mr Bolaji Ogunsanya ne ya tura su Legas daga Amurka domin a bai wa wani “Mr Azeez”.
Lauyan ya bayyana cewa kayan sun isa Legas amma aka neme su aka rasa a tashar jirgin saman.