Rundunar ‘yan sanda ta jihar Borno, ta ce, ta kama wata mata mai suna Fatima Abubakar, bisa zargin kashe mijinta mai suna Goni Abbah ta hanya sanya masa guba a abinci.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Abdu Umar, ne ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labaran kasar (NAN) a Maiduguri babban birnin jihar.
Kwamishinan ya ce marigayin – wanda shi ne limamin unguwarsu – ya dawo daga masallaci ne a lokacin da matar wadda ita ce matarsa ta biyu ta sanya masa guba a abincinsa.
Ya ci gaba da cewa lokacin da marigayin ya fara cin abincin, nan take ya shiga wani mummunan yanayi, inda nan da nan aka ɗauke shi zuwa asibiti domin ba shi kulawar gaggawa, amma daga ƙarshe sai ya rasu.
Matar wadda ke tsare a hannun ‘yan sanda ta shaida wa kamfanin dillacin labaran Æ™asar NAN cewa ta kashe mijin nata ne saboda ta gaji da auren.
Ta kara da cewa ”Bana son auren. Goni shi ne mijina na biyu, na rabu da mijina na farko saboda na tsanbi aure”.