Mataimakin gwamnan jihar Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya yabawa matan jam’iyyar APC, bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabar mata ta jam’iyyar APC ta jihar kano, Hajiya Fatima Abdullahi Dala, wadda ta jagoranci tawagar shugabannin mata da sauran jiga-jigan jam’iyyar a fadin kananan hukumomi 44 da suka kai masa ziyarar taya murna kan lashe zaben fidda gwani na dan takarar Gwamnan kano a jam’iyyar APC.
Cikin Sanarwar da babban Sakataren yada labaran Mataimakin Gwamna Hassan Musa fagge ya aikawa manema labarai, ya ce, ya yi imanin matan da aka san su da aminci, sadaukarwa da jajircewa za su marawa APC baya wajen samun nasara a lokacin babban zabukan shekara ta 2023.
Mataimakin Gwamnan ya umarce su a matsayinsu na Iyaye kuma masu son ci gaba da su ci gaba da koyar da kyawawan dabi’u ga yara ta hanyar basu tarbiyya domin samun al’umma ta gari.
Gawuna ya kuma bayyana cewa an baiwa mata a Kano damammaki Masu yawa saboda gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tana sane da irin rawar da suke takawa, iya karfinsu, wajen samun nasara a zabukan da Suka gabata.
Ya kuma gode musu bisa ziyarar tare da bada tabbacin ci gaba da ba su goyon baya domin samun nasarar jam’iyyar APC. In ji Kadaura.