fidelitybank

Matakin gyara da muka ɗauka ya fara haifar da ɗa mai ido – Tinubu

Date:

Shugaban kasa Bola Tinubu ya nanata kira ga ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri domin akwai haske a gaba, sannan ya ƙara da cewa gwamnatinsa mai sauraron koken jama’a ce.

Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, lokacin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyar fastocin Cocin Katolika ta Catholic Bishop’s Conference of Nigeria (CBCN) a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Ya bayyana wa malaman cocin cewa ya ɗauki matakai masu tsauri bayan ya karɓi mulki a shekarar 2023, ciki har da cire tallafin man fetur.

“Lallai cire tallafin man fetur mataki ne mai tsauri, amma ya zama dole ne domin ba za mu cigaba da jinginar da ƙasarmu ba,” in ji shi, kamar yadda tashar Channels ta ruwaito daga mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga.

“Sai dai akwai alamun nasara da sauƙi a gaba. Ana bayyana abubuwa masu kyau game da Najeriya, kuma ina alfahari da haka. Matakan masu tsauri yanzu sun fara nuna alamomi masu kyau.”

Ya ce damina ta yi albarka wanda hakan ya sa farashin kayan abinci yake sauka, sannan farashin man fetur ma yana sauka.

A game da batun hare-haren ta’addanci, Tinubu ya ce rashin tsaro yana shafar musulmi da kirista, inda ya ƙara da cewa matarsa kirista ce, don haka ba zai zama mai yi musu kisan mummuƙe ba.

leadership newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin ƴan Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...

Isra’ila ta buga gangar yaƙi – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce...

Iran ta na cigaba da luguden makami mai Linzami cikin Isra’ila

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Isra'ila yayin...

Alhazan Najeriya sun fara dawo wa daga ƙasar Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da isowar...

Sojoji sun kama ɗan kasar China da zargin kai wa ƴan Boko Haram kayayyaki

Rundunar sojojin ƙasar nan ta kama wani dan kasar...

Isra’ila ta tsokano tsuliyar Dodo – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce...

Da sani na Isra’ila ta kai hari Iran – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana sane...
X whatsapp