Shugaban ƙasa Bola Tinubu ye ca, matakan da suka ɗauka na inganta tattalin arzikin ƙasar sun fara haifar da ɗa mai ido.
Tinubu ya bayyana haka ne a cikin jawabin da ya gabatar a majalisar dokoki, inda ya ce, “gyare-gyaren da muka yi sun fara haifar da ɗa mai ido.
“Ƴan Najeriya sun kusa fara jin gajiyar ingantaccen tattalin arziki. Ƙasarmu tana samun ci gaba sosai a fagen tattalin arziki.”
Ya ƙara da cewa tattalin arzikin Najeriya ya inganta, inda a cewarsa ya haɓaka da kashi 3.46 a rubu’i na uku na shekarar 2024, daga kashi 2.54 a rubu’i na uku na shekarar 2023.