Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Filato, ya ce gwamnatinsa ta na aiki tare da mahukunta a jihar Kaduna domin sanin abin da za su yi wa dangin matafiyan da aka kashe kwanan baya a jiharsa, waɗanda ƴan asalin Zaria ne.
Gwamnan ya kuma ce rikice-rikice masu nasaba da rashin yardar da ke tsananin mabiya addinai da ƙabilu daban-daban, wanda kuma a wasu lokuta kan ritsa da matafiyan da ba su ji ba, ba su gani ba, ba lallai ne a iya kawo ƙarshensu cikin ɗan lokaci ba.
A hirarsa da BBC, gwamna Mutfwang ya ce sun ɗauki matakan da suka dace a game da kisan mutanen, musamman domin ganin an yi wa iyalan waɗanda aka kashen adalci.