Mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka Kamala Harris, ta isa Tanzania, don ci gaba da ziyarar da take yi ta farko a Afirka.
Za ta gana da shugabar ƙasar Samia Suluhu Hassan, inda ake sa ran za ta taso da batun matsayin Tanzaniyan na ‘yar ba ruwanmu a yakin Ukraine.
Amurka na neman karin ƙasashen da za su yi Alla-wadai da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
Rahotanni sun ce, ziyarar mataimakiyar shugaban na Amurka, ta zo ne a daidai lokacin da sauran manyan ƙasashen duniya kamar Rasha da China ke kokarin yin tasiri a Afirka. In ji BBC.