Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Obarisi Ovie Omo-Agege, ya bayyana cewa, zai tsaya takarar gwamnan jihar Delta a karkashin jam’iyyar APC.
Kafin ya ayyana shiga takarar gwamna, Omo-Agege ya nemi afuwar magoya bayansa sama da dubu goma da suka isa filin wasan kwallon kafa na jami’ar tarayya ta albarkatun man fetur da ke Effurun da misalin karfe 7 na safe, amma an fara shirin ne da misalin karfe hudu na yamma.
Ya ce, duk da zuwa da wuri da magoya bayan, sun ci gaba da hakuri abin da ya ce, alama ce ta APC a shirye take ta fatattaki PDP daga jihar.
Omo-Agege ya ce, zai kawo sauyi a jihar Delta nan da kasa da shekaru hudu, yana mai cewa, ko a matsayinsa sa na Sanata ya yi ayyuka da dama a mazabar sa kuma idan aka zabe shi gwamna zai tabbatar da cewa, an samu ci gaba a gundumomin Sanata uku.
Ya ce, duk alkawurran da ya dauka yayin da ya bayyana tsayawa takarar majalisar dattawa ya cika su.