Ofishin shugaban ƙasar Malawi, ya ce, jirgin sama ɗauke da mataimakin shugaban ƙasar, Saulos Chilima, ya ɓace ba tare da an ji ɗuriyarsa ba.
Sanarwar ta ce, na’ura ba ta ƙara jin ɗuriyar jirgin sojojin ƙasar ta Malawi ba, bayan ya tashi daga Lilongwe, babban birnin ƙasar a safiyar yau Litinin.
Shugaban ƙasar, Lazarus Chakwera, ya bayar da izinin a fara aikin bincike da na ceto, bayan ma’aikatan jiragen sama a ƙasar sun ce, sun kasa yin magana da matuƙan jirgin.
Asali dai jirgin na kan hanyarsa ne zuwa babban filin jirgin sama Mzuzu, da ke arewacin ƙasar, inda ake sa ran zai isa da ƙarfe 11 na safe.
Tuni shugaban Malawi, Lazarus Chakwera, ya soke wata tafiya da ya shirya yi zuwa kasar Bahamas.