Mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na jihar Zamfara, Farfesa Kabiru Jabaka, ya fice daga jam’iyyar.
Ya ce PDP ta rasa alkibla, ya kara da cewa, yanzu ba ta cikin ka’idojin samar da adalci ga al’umma.
A wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Juma’a, Farfesa Jabaka ya ce, ficewar sa daga jam’iyyar ta biyo bayan gudanar da ayyukanta ne ba tare da la’akari da tsarin mulki a jihar ba.
“Mutane da yawa suna tambayar shin da gaske na fice daga PDP kuma mene ne dalilan da kuma ko na yi murabus daga mukamina a jam’iyyar ko a’a kuma mene ne dalili?
“Amsar ita ce tabbatacce kuma amsar da ta gabata ta dace da na ƙarshe.
“Na dauki wannan matakin ne bisa la’akari da cewa PDP ta daina bin ka’idojina wadanda suka dogara da adalci na zamantakewa da ci gaba kamar yadda yake kunshe a cikin kundin tsarin jam’iyyar.
“Sakamakon shugabanni masu kwadayi, jam’iyyar gaba daya ta rasa alkibla,” in ji mataimakin shugaban.
Ya bayyana cewa, jam’iyyar na gudanar da ayyukanta ba tare da la’akari da kundin tsarin mulkin kasa da nata tsarin mulki, ka’idoji ko ma na ado ba. In ji Triump.