Mataimakin Konturola mai kula da gidajen yari a Minna na jihar Neja, ACC Abdulrahman Ibrahim Gegle, wanda wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi garkuwa da shi ya shaki isakr ‘yanci.
An yi garkuwa da ACC Abdulrahman a kan hanyar Ilorin zuwa Minna a ranar 17 ga Afrilu 2024.
Cibiyar ta gyaran hali a cikin wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a Minna, mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a, CSC Rabiu Mohammed Shuaibu, ta ce, Abdulrahman an sake shi ne a safiyar Larabar nan.
Tun a baya dai masu garkuwa da mutanen, sun bukaci a biya su kudin fansa Naira miliyan 25, a lokacin da suka tuntubi iyalansa, kwana guda bayan sace shi a ranar 17 ga Afrilu.