Gwamnatin jihar Kano ta sanar da rasuwar babban mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin gidajen rediyo Abdullahi Tanka Galadanci.
Malam Galadanci ya rasu ne a ranar 26 ga Maris 2025 bayan gajeriyar jinya a asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH).
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana alhininsa game da wannan rashi, inda ya bayyana Tanka Galadanci a matsayin mutum mai kwazo kuma mai kima a gwamnatin wanda irin gudunmawar da ya bayar a kafafen yada labarai da sadarwa na jihar na da matukar muhimmanci.