Kafar yada labaran Rasha ta ruwaito cewa mataimakin gwamnan birnin Kherson Kirill Stremousov – wanda Rasha ta nada – ya mutu a wani hatsarin mota.
An nada Mista Stremousov mai 45 a matsayin mataimakin gwamnan birnin watanni biyu bayan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
Ya kasance daya daga cikin mutanen da suka yi fice a lokacin mamayar, inda ya yi fice wajen fitar da kausasan sakonni a shafukan sada zumunta
‘Yan sanda Ukraine dai sun bayyana nemansa ruwa-a-jallo saboda zargin cin amanar kasa.