fidelitybank

Mataimakin Gwamna ya koma jihar sa ta Ondo a matsyin Gwamna

Date:

Mukaddashin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya koma jihar ne a ranar Laraba, kwanaki biyu bayan ganawarsa da shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Aiyedatiwa ya gana da shugaban kasa da wasu masu ruwa da tsaki kan rikicin siyasar jihar Ondo.

Mukaddashin gwamnan wanda ya sauka a filin jirgin saman Akure a cikin wani jirgin sama na kasuwanci, ya samu tarbar wani jigo a jam’iyyar APC da kuma daraktan kula da harkokin kasuwanci na hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC), Ifedayo Abegunde.

Ya isa jihar ne jim kadan bayan majalisar ta tabbatar da samun wata wasika daga gwamna Oluwarotimi Akeredolu da ke mika masa mulki.

A cikin wasikar, Akeredolu ya kuma bayyana cewa zai tafi hutun jinya.

Idan ba a manta ba rashin gwamnan ya haifar da dagula al’amura a jihar, inda ake kira da a mika mulki ga Aiyedatiwa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Haka kuma, ci gaban ya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin mambobin majalisar zartaswar jihar, inda wasu kwamishinonin suka kafa tantuna tare da Aiyedatiwa.

An kuma yi zargin cewa wasu jami’ai na yin jabun sa hannun gwamnan.

legit.news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp