fidelitybank

Mata na tona gidan Tururuwa don neman abinci a jihar Borno

Date:

Mazauna wasu yankunan jihar Borno da ma’aikatan kiwon lafiya, sun nuna fargaba game da ƙaruwar yara masu tamowa da ake samu a cikin jihar.

Abin da suka ce na da nasaba da rashin wadataccen abinci mai gina jiki ga mata masu shayarwa.

Bugu da ƙari rahotanni sun nuna cewa ƙananan hukumomi bakwai ne a jihar ta Borno, matsalar ta fi shafa.

Ƙananan hukumomin sun haɗa da Marte da Kukawa da Abadam da Guzamala da Kaga da Mobar da kuma Gubio.

Yaran da ke a waɗannan ƙananan hukumomin sun dogara ne kacokam ga tallafin da suke samu daga ƙungiyoyin agaji.

Wata mata da ke aiki a ɗaya daga cikin ƙungiyoyin agajin Fatima Muhammed Habib, ta shaida wa BBC cewa, ada mutane basu san ana fama da wannan matsala ba.

Ta ce,” Da muka je ɗaya daga cikin waɗannan garuruwa mun tarar rabin yaran garin na fama da matsalar abinci mai gina jiki, haka suma matan da ke shayarwa, zaka gansu duk a wahale babu wani abinci mai maiƙo ko kyau da suke samu suna ci ga shi kuma suna shayarwa.”

Fatima Muhammed Habib, ta ce idan har uwa bata ci ta ƙoshi ba ta yaya za ta samu ruwan nono ballantana har ta shayar da ɗanta?.

Ta ce,” Saboda tsagwaron yunwa haka zaka ga mata na tona gidan tururuwa don samu abinci, haka mata ke ƙungiya suna yawo don neman gidan tururuwar da za su samu abinci.”

” Babban abin tashin hankalinma shi ne daji matan ke zuwa don su samo gidan tururuwar, ga rashin tsaro a wuraren ga macizai da dai sauransu.”

Ta ce suna kai musu taimako, amma taimakon ba lallai ya isa ba.

Kungiyar likitoci ta Medicins Sans Frontiers ta fitar da wani rahoto a watan Yuni inda ta ce akwai yara 1,594 da ke fama da ƙarancin abinci mai gina jiki.

Gwamnatin jihar dai ta ce tana ƙokari wajen kawo karshen wannan matsala.

bbc naija news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp