A jihar Taraba, mata mafarauta ne suka bi sahun takwarorinsu maza wajen yaki da ‘yan bindiga a jihar.
Jaridar Daily Trust, ta rawaito cewa matan sun hadar da masu aure da kuma marasa aure.
Matan sun ce sun shiga a dama da su a yakin ne saboda su taimaka wa mazan wajen murkushe ‘yan bindigar da suka addabi jihar.
Matan sun ce, ana kashe mutane maza da mata har da yara a wasu sassan jihar, yayin da ake sace wasu ciki har da matan aure da yammata sannan ayi musu fyade musamman a yankunan Karim-Lamido, da Gassol da kuma karamar hukumar Bali.
Matan sun ce irin wadannan abubuwa da ke faruwa ne ya sa su shiga cikin kungiyar mafarautan da ke yaki da ‘yan bindiga a jihar.
Sun ce suna da kwarin gwiwa kuma ba sa tsoro don haka a shirye suke su shiga cikin yakin da ake da ‘yan bindiga a jihar ta Taraba don murkushe su.