Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA, ta bayyana cewa mata da kananan yara ne suka fi fama da matsalar ambaliya a bana a jihohi 19 da lamarin ya shafa.
Takaddar bayanai na hukumar ta bayyana cewa jihohi biyar ne suka fi yawan mutanen da ambaliyar ta shafa, wadanda suka hada da Imo, Rivers, Abia, Borno da Kaduna.
Bayanai sun bayyana cewa sama da mutane 165 ne suka mutu, 82 sun bace, yayin da wasu 119,791 kuma suka samu raunuka sakamakon ambaliyar.
NEMA ta bayyana hakan ne a cikin dashboard din data a ranar Juma’a.
Hukumar ta ce, “Mutane 138 sun samu raunuka daban-daban, 43,936 suka rasa matsugunansu, gidaje 8,594 da abin ya shafa ya ruguza gonaki 8,278 a fadin kananan hukumomi 43 (LGAs) na Jihohi 19.”
Ya kuma bayyana cewa wadanda ambaliyar ta shafa a sakamakon ambaliyar sun hada da yara 53,314, mata 36,573, maza 24,600, tsofaffi 5,304, da kuma nakasassu 1,863.
Ya bayyana cewa Abia, FCT, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Borno, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Kogi, Kwara, Niger, Ondo, Rivers da Sokoto sune jihohi 19 da ambaliyar ta shafa.