Wasu dalibai mata hudu da aka yi garkuwa da su na kwalejin fasaha da kimiya ta jihar Zamfara, ZACAS, Gusau, sun samu ‘yanci bayan shafe sama da watanni shida a cikin gidan ‘yan bindiga.
Masu garkuwa da mutane sun fitar da wasu faifan bidiyo guda biyu a lokuta daban-daban, inda aka ga wadanda lamarin ya shafa na kuka da neman agaji daga gwamnati da masu hannu da shuni don neman ‘yancinsu.
Daya daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su ta rasa mahaifiyarta wacce ta mutu saboda kaduwa bayan ta kalli faifan bidiyo na farko.
An yi garkuwa da su ne a hanyar Bimini Magaji-Laura Namoda a watan Janairu, 2023, yayin da suke dawowa daga wani bikin aure.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da cewa jami’an tsaro a jihar sun ceto su.


