Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bukaci masu zuba jari na cikin gida da na waje da su ci gajiyar sabbin damammaki da karancin wutar lantarki ya haifar a kasar nan.
Shettima ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin din da ta gabata, a wajen bude taron bayar da kudi na mayar da kamfanin samar da wutar lantarki na kasa guda biyar, NIPP, Plants a Abuja.
Mataimakin shugaban wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa (Ofishin mataimakin shugaban kasa), Sen. Ibrahim Hadejia, ya ce taron ya kasance tabbaci ne ga ‘yan kasuwa da kuma fara saka hannun jari tare da samun riba mai kyau.
Ya jaddada bukatar masu zuba jari su yi amfani da damar da gwamnatin tarayya ke yi na kara zuba jari a bangaren makamashin Najeriya.
Shettima ya kuma yi alkawarin daukar nauyin gwamnatin shugaba Bola Tinubu na magance matsalar karancin makamashi a kasar, inda ya kara da cewa gwamnati ta mayar da hankali wajen inganta harkokin kasuwanci.
“Rashin wutar lantarki a Najeriya yana ba da gayyata ga abokan huldar gida da waje. Muna nan don ƙarfafa ƙoƙarin haɗin gwiwa don samar da mafita mai dorewa.
“Gwamnati ta tsaya tsayin daka wajen magance karancin makamashi kuma ta mai da hankali kan inganta saukin kasuwanci.
Mataimakin shugaban kasar, duk da haka, ya bukaci masu son zuba jari da su “dauki nauyin amana wajen amfani da wadannan albarkatun domin amfanin kasa,” in ji shi.